An kashe sama da mutane 10 a harin kunar bakin Wake a kasar Mali
Wani harin da masu goyon bayan gwamnati da suka hada da ‘yan kunar bakin Wake suka kai a yankin Arewacin Mali, ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 10 kai tsaye
Wallafawa ranar:
Wata majiyar jami’an tsaro ta ce mayakan na GATIA ne tare da wasu ‘yan kunar bakin wake suka kai harin ga ‘yan tawaye masu adawa da gwamnatin kasar Larabawa a kusa da garin Tabankort.
Haka ma an ce an kashe wasu mutane 3 a wata zanga-zangar da aka yi ta kalubalantar Majalisar dunkin Duniya.
Wata majiyar jami’an tsaro a MINUSMA ta ce Rundunar Dakarun tsaro na Majalisar dunkin Duniya a Mali ta tabbatar da kisan, ta kara da cewar wasu mahara biyu sun tarwatsa kansu a yayin da aka kashe na 3 kamin ya iya tarwatsa kansa.
An dai tilastawa Dakarun Majalisar dunkin Duniya ficewa ne, a wani matakin kirkiro sansanin Jami’an tsaro na wuccin gadi a Tabankort, bayan wata yarjejeniya da aka yi a yankin Arewacin birnin bao, da aka ce wasu masu goyon bayan gwamnati suka shirya.
An kuma kashe wasu mutane 3 a ran Talata, rana ta 2 da aka gudanar da zanga-zangar kyamar Dakarun Majalisar dunkin Duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu