Somalia
Somalia ta dauki matakan yaki da Ebola
Gwamnatin kasar Somalia ta yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa wani mutumin ya shigo da cutar Ebola a cikin kasar daga Guinea. Gwamnatin kasar ta yi wa al’ummar kasar alkawarin daukar matakan da suka dace don kaucewa bullar Ebola a cikin kasar.
Wallafawa ranar:
Talla
Ministan lafiya Ali Mohamed Mohamud ya shaidawa manema labarai cewa suna kula da lafiyar mutumin da ake zargin yana dauke da Ebola mai suna Abdulkadir tare da duk mutanen da suka yi mu’amula da shi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu