Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar tsaron Najeriya tana tsare da jirgin kasar Rasha da ya dauko makamai

Rundunar tsaron Nigeria tace tana tsare da wani jirgin saman daukar kaya na kasar Rasha, da ya dauko kayan yaki irin na Soja, ya kuma sauka a birnin Kano. Jirgin na kuma dauke da wasu mutane ‘yan kasashen Rasha da Faransa, lamarin da ha haddasa cecekuce a kasar.Cikin sanarwar da suka sanya ta dandalin sada zumunta na Twitter, shugabanin rundunonin tsaron Nigeria sun ce ana ci gaba da bincike kan kayayyakin da ke cikin jirgin, da yayi saukar bazata a birnin Kano dake arewacin kasar.‘Yan Nigeria da dama sun yi ta yin hasashe daban daban kan makasudin zuwan jirgin a Nigeria, ganin yadda aka dade ana zargin hannun wasu kasashen waje, a ayyukan kungiyar nan ta Boko Haram.Da farko ofishin Jakdancin kasar Rasha Nigeria ya nesanta kasar da Jirgin, sai dai kuma daga baya ya amincea da cewa na kasar ne, amma yana duke ne da kayan yakin kasar Faransa.Shima jakadan Faransa a Nigeria Jacques Champagne de Labriolle, yace jirgin na dauke ne da kayan aikin sojan da aka kwashe daga kasar Jamhuriyar Africa ta Tsakiya, inda sojan na Faransa suka kawo karshen aikin su, kuma za a kai sune zuwa Chadi, inda sojan ke kokarin murkushe ‘yan tawayen yakin yammacin Africa. 

Jirgin kasar Rasha da aka kama dauke da makamai a Kano, Nigeria
Jirgin kasar Rasha da aka kama dauke da makamai a Kano, Nigeria
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.