Taron Majalisar Dinkin Duniya a New York
Shugaban Amurka Barack Obama da kuma shugabannin manyan kasashen duniya za su gabatar da jawabai a gaban babban taron zauren majalisar dinkin duniya a birnin New York. Kwana daya bayan da Amurka da kawayenta suka kaddamar da hare-hare akan mayakan jihadi a cikin kasar Syria.
Wallafawa ranar:
Har ila yau shugaba Obama zai jagoranci wani taron musamman na kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, domin samar da kudurin da zai hana kwararar mayakan jihadi zuwa kasashen da ke fama da ‘yan bindiga.
To sai dai ba dukkanin kasashe masu kujerun dindindin a Majalisar ne ke goyon bayan salon fada da ta’addancin da Amurka ke jagoranta a Iraki da Syria ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu