Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam’iyyar APC ta lashe zaben Osun

Gwamna mai ci kuma Dan takarar jama’iyyar APC a zaben Jihar Osun Rauf Aregbesola, ya lashe zabe da aka yi jiya Assabar, inda ya sami jimillar kuri’u 394,684 fiye da Dan takarar Jam’iyyar PDP Sanata Iyiola Omisore.

Gwamnan Jihar Osun Engineer Rauf Aregbesola
Gwamnan Jihar Osun Engineer Rauf Aregbesola Osun.gov
Talla

‘Yan takarar Gwamna daga Jam’iyyu 20 ne suka fafata a Zaben da aka gudunar a Jihar Osun. Kuma Gwamna Mai ci Aregbesola ya lashe zaben ne a kananan hukumomi 24 daga cikin 30 da ake da su a cikin Jihar.

Dan Takatar Jam’iyyar PDP Iyiola Omisore, shi ne ya zo a matsayi na biyu a zaben da yawan kuri’u 292,750 inda ya samu nasara a kananan hukummoi guda shida.
Fatai Akinbade na Jam’iyyar labour shi ne ya zo a matsayi na uku.

Amma zaben ya fi daukar hankali tsakanin ‘Yan takarar Jam’iyyar APC mai adawa a Tarayya da kuma PDP mai mulki a Najeriya.

Tuni dai shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya mika sakon taya murnarsa ga Aregbesola, akan nasarar da ya samu a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.