Faransa zata baza dakaru a Sahel
Gwamnatin Faransa tace Sojojinta da suka kwato arewacin Mali zata baza su a Sahel domin dakile ayyukan ta’addanci a yankin, kamar yadda Ministan tsaro Jean-Yves Le Drian ya tabbatar a wata tattaunawa a kafar Telebijin.
Wallafawa ranar:
A watan Janairun bara ne Faransa ta aika da dakaru domin taimakawa Sojojin Mali kwato yankin arewaci da ya fada ikon ‘Yan tawayen Abzinawa da Mayakan MUJAO.
Ministan tsaron Faransa yace nan ba da jimawa ba ne Sojojin zasu kaddamar da yaki a Sahel tare da hadin gwiwar kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da Chadi da Mauritiania.
Le Drian yace kimanin Sojojin Faransa 3,000 ne zasu yi aiki a yankin Sahel, yayin da Sojoji 1,000 za su ci gaba da kula da sha’anin tsaro a Mali.
Sojojin kuma zasu yi amfani da manyan jiragen sama da kanana da wadanda ke tuka kansu da tankokin yaki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu