Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Pistorius na cikin hayyacinsa lokacin da ya harbi Reeva

Likitoci da suka gudanar da bincike kan zakaran duniya na tseren gudun kafa na nakasassu Oscar Pestorius, sun ce yana a cikin koshin lafiya lokacin da ya harbe masoyiyarsa Reeva Steenkamp a shekarar da ta gabata.

Oscar Pistorius, zakaran gudun kafa na nakasassu a duniya.
Oscar Pistorius, zakaran gudun kafa na nakasassu a duniya. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Yau litinin ne likitoci suka gabatar da rahotonsu a gaban kotun da ke ci gaba da yi wa Pestorius shari’a, bayan da suka share tsawon wata daya suna gudanar da bincike domin tantance ko yana fama da tabin hankali ne lokacin da ya aikata kisan.

Pestorius, dan kimanin shekaru 27 a duniya, an soma gudanar da shari’arsa ne tun ranar 3 ga watan maris da ya gabata a birnin Pretoria, kuma matukar dai aka same shi da laifi ana iya yanke masa hukuncin daurin rai da rai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.