Masar: Kotu ta yanke wa ‘Yan Uwa Musulmi 183 hukuncin kisa
Wata kotu a kasar Masar ta tabbatar da hukuncin kisa akan mambobin Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi 183 cikinsu har da Shugabansu Mohammed Badie, bayan kotun ta kama su da laifin kisan wasu ‘Yan sanda guda biyu a garin Minya a watan Agusta.
Wallafawa ranar:
Wannan kotun ce a Minya ta yanke wa Mutane 683 hukunci kisa a watan Afrilu, hukuncin da ya janyo suka daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama.
A ranar 14 ga watan Agusta ne aka kashe wasu ‘Yan sanda guda biyu a Minya, ranar da kuma ‘Yan sanda suka kashe daruruwan magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohammed Morsi a birnin al Kahira.
Tun lokacin da Sojoji suka hambarar da gwamnatin Morsi a watan Yuli, aka kaddamar da farautar mabiya Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi tare da yanke masu hukuncin kisa.
Kotun ta yanke hukuncin ne a yau Assabar kuma akwai mutane hudu da aka sassautawa hukuncin zuwa daurin rai da rai da suka hada da mata guda biyu. Kotun kuma ta wanke wasu mutane 496, kamar yadda mai gabatar da kara Abdel Rahim Abdel Malik ya tabbatarwa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa.
A zaman kotun, an haramtawa ‘Yan Jarida halartar sauraren karar da aka yankewa daruruwan mutanen hukunci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu