Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Najeriya sun yi jimamin mutuwar Ado Bayero

Dubun dubatar mutanen Najeriya sun yi jimamin rasuwar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero daya daga cikin manyan Sarakunan Hausa a Arewain Najeriya wanda ya rasu kuma aka yi Jana’izarsa a ranar Juma’a.

tururuwan Mutane  a lokacin Jana'izar Sarkin Kano alhaji Ado Bayero wanda ya rasu a ranar Juma'a 6 ga watan Yuni 2014
tururuwan Mutane a lokacin Jana'izar Sarkin Kano alhaji Ado Bayero wanda ya rasu a ranar Juma'a 6 ga watan Yuni 2014 REUTERS/Stringer
Talla

A ranar Juma’a ne Allah ya yi wa Mai Martaba Ado Bayero rasuwa wanda ya kwashe shekaruu 51 yana sarauta a Kano.

Shugaban Najeriya goodluck Jonathan yace rasuwar Ado Bayero, Najeriya ce ta yi rashin daya daga cikin Sarakunan da ake girmamawa a kasar.

Dubban mutanen Kano ne suka yi tuturuwa a wajen Jana’izar Marigayi Ado Bayero.

Yanzu batun da ke zukatan ‘Yan Najeriya musamman Kanawa shi ne wanda zai gaji Ado Bayero. 

Masu zabar Sarki a Masarautar Kano zasu mika sunayen mutane uku ‘Yan jinin sarauta zuwa ga gwamnan Kano wanda zai zabi cikinsu sabon Sarkin da zai gaji Ado.

Cikin mutanen uku da za’a zaba ana sa ran har da Tsohon Gwamman babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi wanda jika ne ga Tsohon Sarkin Kano Sanusi.

Akwai kuma Aminu Ado Bayero Hakimin Dala, da kuma Hakimin Karamar hukumar Gwale, Alhaji Ciroma Lamido Ado Bayero, da  Nasiru Ado Bayero wadanda cikinsu ake sa ran wani zai gaji Mahaifinsu a matsayin Sarkin Kano.

01:30

Rahoton Abubakar Isa Dandago daga Kano

Abubakar Issa Dandago

Akwai manyan ‘Yan siyasa da tsoffin Shugabannin kasa da kuma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na Uku da suka halarci Jana’izar Ado Bayero a lokacin da za’a binne gawarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.