Isa ga babban shafi
Najeriya

An gano gida shake da sassan jikin mutane a Ibadan Najeriya

Rundunar ‘yan sandar Najeriya ta sanar da gano wani gida shake da kasusuwa, kawuna da kuma gabobin mutane a garin Ibadan da ke yankin kudu maso yammacin kasar.

Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya
Goodluck Jonathan, shugaban Najeriya
Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Oyo Olabisi Ilobanofor, ya tabbatar da wannan labari, inda ya ce jami’ansa sun shiga a cikin gidan, kuma sun tarar da kasusuwa da kuma sassa daban daban na jikin dan adam.

Har ila yau jami’in ‘yan sandar ya ce an tarar da wasu mutane da rayukansu a cikin gidan, to sai dai bisa ga dukkan alamu sun share dogon lokaci ba tare da an ba su abinci ba, kuma ‘yan sanda sun kaddamar da bincike akan wannan lamari.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.