Shugaban Senegal Macky Sall na ziyarar aiki a China
Shugaban kasar Senegal Macky Sall na gudanar da ziyarar aiki a kasar China daga yau laraba, kuma wannan shi ne shugaban Afirka na farko da Xi Jinping ya gayyata zuwa birnin Beijing tun daga lokacin da ya dare kan karagar mulki.
Wallafawa ranar:
A 2005 ne Senegal ta sake kulla huldar diflomasiyya da China bayan da ta share tsawon shekaru 10 tana alaka da kasar Taiwan wadda China ke kallo a matsayin wani yankin da ke karkashin ikonta.
Akwai dai alakar kasuwanci da ta kai ta Euro milyan 600 tsakanin Senegal da China, yayin da kamfanoni da kuma gwamnatin China ke da hannayen jari da dama a al’amurran da suka shafi hako ma’adinai a Senegal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu