Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Kiir da Machar sun amince su aika da wakilai zuwa Habasha

Bangarorin da ke rikici da juna a kasar Sudan ta kudu sun ce a shirye suke su aika da wakilainsu zuwa birnin Addis Ababa a kasar Habasha domin gudanar da tattaunawar sulhu bayan shafe sama da mako biyu ana gwabza fada tsakanin dakarun da ke biyayya ga Reik Machar da dakarun shugaba Salva Kiir.

Shugaban kasar sudan ta Kudu Salva Kiir da Yoweri Museveni, à birnin Juba
Shugaban kasar sudan ta Kudu Salva Kiir da Yoweri Museveni, à birnin Juba AFP PHOTO/ SAMIR BOL
Talla

Shugabannin kungiyar kasashen gabacin Afrika ne ta IGAD zasu jagorantanci zaman tattaunawar ta sulhu tsakanin bangarorin biyu amma har yanzu babu tabbas game da lokacin da za’a shiga tattaunawar.

Kakakin gwamnatin Sudan ta Kudu, Michael Makuei ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP cewa har yanzu shugaba Salva Kiir be fadi sunayen wadanda za su wakilce shi ba a zaman tattaunawar a Addis Ababa, amma yace shugaban a shirye ya ke ya aika da wakilansa.

Haka ma a bangaren tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar, kakakinsa Moses Ruai yace suna jiran wakilan kungiyar IGAD ne domin kama hanyar zuwa birnin Addis Ababa.

Manufar farko da kungiyar kasashen gabacin Afrika ke kokarin cim ma ita ce ta tsagaita wuta kafin a tsunduma cikin sauran batutuwan siyasa da bangarorin biyu suka sabani akai.

Tun a ranar 15 ga watan Disemba ne rikici ya barke a Sudan ta kudu bayan da shugaba Kiir ya zargi Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa, zargin da kuma ya musanta yana mai zargin Kiir da kokarin karya ‘yan adawa.

Rikicin yanzu ya bazu zuwa wasu sassan yankunan kasar inda dakarun Machar suka karbe ikon garin Bor babban birnin Jahar Jonglei.

Alkalumman Majalisar Dinkin duniya sun ce daruruwan mutane ne aka kashe a rikicin na mako biyu yayin da wasu da dama suka gujewa gidajensu bayan da rikicin ya rikide zuwa na kabilanci tsakann kabilar Dinka ta shugaba Kiir da kuma kabilar Nuer ta Machar.

Tuni Machar ya yi watsi da duk wani mataki na tsagaita wuta yana mai cewa sai ya gamsu da sakamakon tattaunar da za’a yi a Addis Ababa tare da yin watsi da duk wani mataki na yin gaba da gaba da Shugaba kiir.

Sai dai kuma Babban kwamandan dakarun SPLM Choul Laam, a hirar shi da Rediyo Faransa yace, ya yi imanin idan har Shugaba Salva Kiir da Riek Machar suka zauna a daki daya suka tattauna, za a sami mafita game da wannan rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.