Isa ga babban shafi
Somaliya-MDD-KTA

Majalisar Dinkin Duniya zata kara yawan dakarunta a kasar Somaliya

Komandan dakarun Kungiyar kasashen Afrika dake aikin samar da zaman lafiya a kasar Somalia, Brig Dick Olum, yace karin sojojin da Majalisar Dinkin Duniya zata tura a kasar, zasu yi aikin kaddamar da hare hare kan kungiyar Al Shebaab ne.

Dakarun kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somaliyae (Amisom), a ranar 11 janvier 2013 a garin  Shabelle.
Dakarun kungiyar tarayyar Afrika a kasar Somaliyae (Amisom), a ranar 11 janvier 2013 a garin Shabelle. REUTERS/Tobin Jones
Talla

Kwamandan yace, karin sojoji 4,000 da Majalisar Dinkin Duniya zata kai a shekara mai zuwa, zai basu karfin kaddamar da hari dan murkushe kungiyar ta Al Shebaab.

Ya zuwa yanzu dai dakarun kungiyar kasashen Afrika da Majalisar Dinkin Duniya 22,000 ke kasar ta Somalia.

Kungiyar Alshabab a kasar Somaliya dai ta zama babbar barazanar samar da zaman lafiya a kasar da ta share tsawon shekaru sama da 20 tana fama da yakin basasa, haka kuma kungiyar ta zama barazana ga kasashen dake makwabtaka da kasar ta Somaliya, inda ta sha daukar nauyin kai hare haren da suke yin sanadiyar hasarar rayukan jama’a a kasar Kenya
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.