Isa ga babban shafi
Mali

Kotu ta tabbatar da zaben IBK a matsayin shugaban kasar Mali

Kotun tsarin mulkin kasar Mali, ta tabbatar da zaben Ibrahim Boubacar Keita a matsayin shugaban kasar, inda ta tabbatar da cewa ya lashe zaben kasar da gagarumin rinjaye.

Ibrahim Boubacar Keïta Sabon Shugaban kasar Mali
Ibrahim Boubacar Keïta Sabon Shugaban kasar Mali REUTERS/Joe Penney
Talla

A ranar 11 ga wannan watan na Augusta ‘yan kasar suka kada kuri’a a zaben zagaye na biyu.

Kotun ta ce Ibrahim Boubacar Keita, ko IBK a takaicece na da kashi 77.6 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin da abokin takarar shi, kuma tsohonm ministan kudi Soumaila Cisse, ya sami sauran kashi 22.4.kashi 45.7.

Wannan ya tabbatar da alkaluman wucin gadin da ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta bayar.

Abokin takarar IBK, Soumaila Cisse ya ce zaben cike yake da magudi, sai dai ya ce ba zai shigar da kara a kotu ba, bayan da ya riga ya amshi kaye.

Ya ce ya yanke shawarar hakan ne domin ganin an sami nasarar fidda kasar daga halin da ta shiga, bayan da juyin mulki.

A halin da ake ciki kuma Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya aikawa sabon shugaban sakon taya murna, inda ya lashi takobin aiki tare da shi, don farfado da kasar ta Mali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.