Isa ga babban shafi
Masar-MDD

Ban Ki-moon ya yi kiran a hau Teburin sasantawa a Masar

Sakatare Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira ga bangarorin kasar Masar su rungumi hanyar zama teburin sasantawa, a daidai lokacin da aka yi mummunan artabu tsakanin jami’an tsaro da kuma magoya bayan hambararren shugaban kasa Mohammad Morsi a birnin Alkahira.

Dubban magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi suna zanga-zanga a birnin al Kahira
Dubban magoya bayan hambararren shugaban Masar Mohamed Morsi suna zanga-zanga a birnin al Kahira REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Ban Ki-moon ta hannun mai Magana da yawunsa Martin Nerisky, ya ce ya yi matukar damuwa dangane da yadda lamurra ke tafiya a kasar ta Masar, yana mai cewa dukkanin bangarorin biyu ne ya kamata su yi wa juna sassauci domin shawo kan wannan rikici da ke tauye kasar Masar da kuma kasashen yankin a cewarsa.

Dubban magoya bayan Morsi ne suka ci gaba da gudanar da zanga-zanga a sassan yankunan Masar suna masu yin wasti da gargadin gwamnati na barazanar watse sansaninsu.

Bayan kammala sallar Juma’a ne bagoya bayan Morsi suka kaddamar da sabuwar zanga-zanga bayan sun huta na kwanki biyu saboda bukukuwan salla.

A lokacin da ya ke jawabin goron Salla, Shugaban gwamnatin Musulunci a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi gargadin cewa Masar na iya abkawa cikin yakin basasa bayan Sojoji sun hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi.

Ya zuwa yanzu dai sama da mutane 250 ne suka mutu tun tunbuke Morsi a ranar 3 ga watan Yuli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.