Isa ga babban shafi
Mali

‘Yan tawayen Abzinawa sun mara wa Kaita baya a zaben Mali

Kungiyar ‘Yan tawayen MNLA wadda a baya ke neman ‘yancin yankin arewacin Mali, a ta bakin jagoran tawagarta a tattaunawar sulhun da aka yi tsakaninta da gwamnati Ibrahim Ag Mohamed Assaleh, ta bayyana goyon bayanta ga Ibrahim Boubakar Keita a zaben shugabancin kasar da za a gudanar a ranar lahadi mai zuwa zagaye na biyu.

Shugaban Burkina Faso, Blaise Compaoré, tare da Shugaban Mayakan Ansar Dine, Alghabass Ag a Ouagadougou.
Shugaban Burkina Faso, Blaise Compaoré, tare da Shugaban Mayakan Ansar Dine, Alghabass Ag a Ouagadougou. AHMED OUOBA / AFP
Talla

Shugaban yace a wurinsu shi ne ya fi dacewa wajen biyan bukatunsu, saboda Kaita ya fi to ne daga cikin kabilar Mandeng, sabanin Soumaila Cisse wanda suka ce saboda dalilai ko an zabe shi, ba zai iya warware rikicin da ake fama da shi tun daga shekarar 1963 zuwa yau tsakanin Arewaci da kuma sauran yankunan kasar ba.

‘Yan tawayen Abzinawan sun ce Mutanensu na arewa, sun sha jefa kuri’unsu ga sauran ‘yan siyasar da suka gabata, bisa zaton cewa za a warware masu matsalolin da suke fama da su a tsawon shekarun, amma shugaban yace har zuwa yau ba a samu wanda zai kawo karshen matsalar ba.

‘Yan tawayen Abzinawa tare da mayakan Ansar Dine da MUJAO sun karbe ikon yankin arewaci ne a bara bayan da Sojoji suka kifar da gwamnatin Amadou Toumani Toure a watan Maris.

A karshen mako ne za’a shiga zagaye na biyu a zaben shugaban kasa a Mali tsakanin Boubakar Kaita da Soumaila Cisse

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.