Isa ga babban shafi
Congo-Uganda

Dubban Mutane Congo sun fice zuwa Uganda

Akalla mutane 23,000 ne suka fice daga birnin Kamango da ke gabacin Jamhuriyyar Conco zuwa Uganda bayan ‘Yan tawaye sun karbe ikon yankin kafin daga bisani su fice. Hukumar ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tace mutanen sun fice ne bayan da ‘Yan tawayen Uganda na ADF sun kai hari a Kamango.

Wata Uwa dauke da 'Yarta a sansanin 'Yan gudun hijira a Kamwenge yammacin Uganda
Wata Uwa dauke da 'Yarta a sansanin 'Yan gudun hijira a Kamwenge yammacin Uganda AFP/File, Michele Sibiloni)
Talla

Wani Jami’in ‘Yan sanda Denis Namuwooza, ya shaidawa AFP cewa kimanin mtane 3,000 ne suka fice zuwa Bundibugyo da ke yammacin Uganda a ranar alhamis kafin sauran adadin mutanen su bi sahunsu a ranar Jum’a.

Akwai dai rahotanni masu karo da juna da ke cewa ‘Yan tawayen sun fice daga Kamango amma kuma wasu Rahotannin na cewa ‘Yan tawayen suna nan suna ci gaba da gallazawa mazauna garin.

A shekarar 1990 ne aka samu bulluwar ‘Yan tawayen ADF a tsaunin Rwenzori da ke yammacin Uganda, kusa da iyaka da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.