Isa ga babban shafi
Najeriya-China

Ziyarar Jonathan na Najeriya a China

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya gana da takwaransa na China Xi Jinping a Beijing a wata ziyara da shugaban ya kai domin inganta huldar kasuwanci tsakanin kasashen biyu. Goodluck Jonathan yana ziyarar ne tare da rakiyar jami’an gwamnatinsa 19.

Wata ma'aikaciya a fadar gwamnatin China dauke da tutar Najeriya a ziyarar da Goodluck Jonathan ya kai a China
Wata ma'aikaciya a fadar gwamnatin China dauke da tutar Najeriya a ziyarar da Goodluck Jonathan ya kai a China REUTERS/Kim Kyung-Hoon
Talla

“ saboda ci gaban tattalin arzikin China ne ya sa na kwaso tawagar Ministocina da dama” Inji Jonathan a lokacin da ya ke ganawa da shugaba Xi.

Kamfanonin China da dama ne ke aikin kwangilar hanyoyi ta kudi da suka kai Dalar Amurka Biliyan 1.7 a Najeriya

Ana sa ran Najeriya za ta samu bashin kudi da suka kai Dala Biliyan 1.3 a ziyarar Jonathan. Kuma ana sa ran Gwamnatin China za ta linka bukatar danyen Mai da take samu a Najeriya daga ganga 20,000 zuwa ganga 200,000 a rana, har zuwa shekarar 2015.

Akwai dai yarjeneniya guda biyar da kasashen biyu suka amince da ita kafin ganawar Jonathan da Xi da suka hada yarjejeniya tsakanin Bankin ci gaban China da kuma First Bank na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.