Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Arch Bishop Desmond Tutu ya lashe kyautar Mo Ibrahim ta shugabanci nagari

Gidauniyar, Mo Ibrahim dake karramashugabanin kasashen Afrika da suka gudanar da mulki na gaskiya, kuma suka sauka ba tare haifar da matsala ba a kasashen su, ta bayyana Arch Bishop Desmond Tutu na kasar Afrika ta kudu, a matsayin wanda ya lashe kyautar ta bana, mai dauke da tsabar kudi Dala miliyan biyar, da kuma Dala 200,000 a kowacce shekara har ya bar  duniya.Attajirin Mo Ibrahim yace an baiwa Tutu kyautar ne saboda rawar da ya taka wajen fadin gaskiya ga shugabanin kama karya. 

Arch Bishop Desmond Tutu
Arch Bishop Desmond Tutu Reuters/Mark Wessels
Talla

shidai Archbishop Desmond Tutu, an haife shi ne a shekarar 1931 a garin Transvaal, dake kasar Afrika ta kudu, inda yayi karatun sa, kana kuma ya bi sahun mahaifin sa, a matsayin malamin makaranta.

Ya bar malaman ta ne a shekarar 1953, lokacin da gwamnatin wariyar jinsi ta Afrika ta kudu ta kafa wata doka, na ware dalibai fararen fata da bakake, abinda ya sa shi ya koma aikin mujami’a, kuma yayi farin jinni wajen shugabanin mujami’a fararen fata, musamman Bishop Trevor Huddleston.

Arch Bishop Desmond Tutu ya zama bakar fata na farko da ya zama Dean a Johannesburg, a shekarar 1975, kafin tashin hankalin da akayi a Soweto, a 1976, abinda ya sa ya kaddamar da yakin neman kawo sauyi kan yadda ake tafi da kasar.

Bukatar san a kawo sauyi da kuma dai daito, ya sa shi mu’amala da siyasa, amma ko da yaushe ya kan ce shi addini ya sa a gaba, ba wai siyasa ba.

An dai zabe shi a matsayin Arch Bishop a shekarar 1986, a matsayin shugaban darikar Anglican, kuma bakar fata na farko.

A shekarar 1988, ya kadadmar da shirin adawa da manufofin gwamnati, kana watanni shida bayan haka, aka kusan daure shi, saboda ya bukaci kauracewa zaben kanana hukumomi.

Tutu ya yaba da matakin da shugaba Frederick de Clark ya dauka a shekarar 1989, na sauye sauyen siyasa, matakin da ya kai ga sakin Nelson Mandel adaga gidan yari.

A shekarar 1995 Mandela ya nada Tutu a matsayin shugaban kwamitin sasanta Yan kasar.

Daya daga cikin abinda ya sashi fice, shine fadin gaskiya, musamman lokacin mulkin turawa, da kuma lokacin da shugaban Amurka na wancan lokaci, George Bush da Prime Ministan Britaniya, Tony Blair suka jagoranci duniya wajen abkawa Iraqi, abinda ya sa aka bashi kyautar Nobel ta duniya.

A ranar lahadi mai zuwa ne zai cika shekaru 81 a duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.