Kotun Burundi ta yanke wa Dan Jaridar RFI hukuncin dauri rai da rai
Hassan Ruvakuki, ma’aikacin Radiyo Faransa RFI a Sashen Swahili yana cikin Mutane 13 da kotun Burundi ta yanke wa hukuncin daurin Rai da Rai a gidan Yari bayan samun shi da laifin zantawa da ‘Yan Tawaye. Ruvakuki yace zai daukaka kara domin kalubalantar hukuncin kotun
Wallafawa ranar:
Dan Jaridan yana aiki ne a matsayin wakilin Sashen Swahili na Radio Faransa, da tashar Bonesha FM a Bujumbura.
Gidan Radio Faransa da Kungiyar Reporters Without Borders, sun bayyana kaduwarsu da hukuncin.
Ruvakuki wanda dan asalin kasar Burundi ne, Kotun ta kama shi da laifin taimakawa ‘Yan Tawayen Burundi a Tanzania bayan Cafke shi aBujumbura babban birnin Burundi a watan Nuwamban Bara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu