Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeria ta cika shekaru 50

Yau juma’a daya ga wata Octoba na shekara ta 2010, tarayyar Nigeria ke gudanar da gagarimin biki da shagulgulan cikar kasar shekaru hamsin da samun ‘yancin kai.Su dai wadannan bukukuwa da aka ware wa zunzurutun kudi Naira miliyan dubu goma, ana gudanar da su ne a daidai lokacin da takaddamar siyasa ke kara kamari, musamman ma kan batun nan na karba-karba ta mulki tsakanin kudu da arewacin kasar.Haka kuma wadannan bukukuwa sun sun zo a yayin da talakawan kasar ke cikin halin Ni- ‘yasu na kuncin rayuwa, da rashin rashin ababen more rayuwa,kana da tabarbarewar al’amura musamman ma dai harkar tsaro, don haka akasari ke ganin babu wani ci gaba da aka samu sai irin na mai hakan rijiya.Duk da cewa wasu ‘yan Nigeria sun yi ta suka dangane da wadancan makudan kudade da suke ganin za a salwantar da su ne kawai a yayin bikin, hukumomi sun yi kunnen uwar shegu, inda a babban birbin kasar aka gunadar da fareti na masu damara iri daban-daban. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.