Isa ga babban shafi
Najeriya

An Rantsar da Goodluck Jonathan a Matsayin Shugaban Kasa

Yau an rantsar da Mukaddashin shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, a matsayin shugaban kasa, bayan rasuwar shugaba Umaru Musa Yar’adua.Yayin da yake jawabi bayan karbar rantsuwar, shugaba Jonathan, ya mika sakon ta’aziya wa iyalan Tsohon shugaban, da kuma daukacin Yan Nigeria, inda yake cewa ya rasa maigida da kuma aboki.Shugaba Jonathan yace, gudumawar da Yar’adua ya bayar wajen tafida Nigeria, bashi misaltuwa, saboda gaskiyar sa, imani da kuma kaskantar da kai, wajen ganin Nigeria ta cigaba.Yayin da yake baiyana nauyin da aka dora masa a matsayin mai girma, shugaban ya sake jaddada bukatarsa na Yaki da Cin hanci da rashawa, sauyin dokar zabe, dan ganin an kirga kuri’ar kowa, kana kuma da tsaro a Yankin Niger Delta, da kuma daukacin kasar. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.