Shirye-shirye

Fasalin kanun labarai

  • Al'adu

    Kawo al’adu na zamani da wadanda suka shude daga sassan kasashen duniya domin mai sauraro ya san cewa, duniyarmu tana da girma da yawan jama’a masu al’adu daban-dabam. Muna kawo maku shirin a ranar Talata shirye-shiryenmu na safe karfe 7:00 agogon Najeriya tare da maimaici a shirin karfe 8:00. Akwai kuma Shirin al'adunmu na musamman na karshen mako da mu ke gabatarwa a ranakun Asabar da lahadi.

  • Bakonmu a Yau

    Bakonmu a Yau

    A kullum mukan gayyaci masana a fannoni daban dabam domin tattauna wasu muhimman al'amurra da suka shafi kanun labarai a duniya.

  • Duniyarmu A Yau

    Duniyarmu A Yau

    Shirin Duniyarmu A Yau, wani dandali inda ‘Yan Jaridu daga kafofin yada labarai daban-daban, ke tattaunawa tare da tafka mahawar kan al’amurran da ke faruwa a kasashen duniya, da batutuwan da suka shafi al’umma kai tsaye, wanda Bashir Ibrahim Idris ke jagoranta.

  • Fina-Finai

    Fina-Finai

    Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayarwa masu sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya baiwa ...

  • Ilimi Hasken Rayuwa

    Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu ta sha'anin Ilimi a fannoni daban-dabam a duniya, tare da nazari ga irin ci gaban da aka cim ma wajen binciken kimiya da ...

  • Kasuwanci

    Shiga kasashen duniya tare da kawo bayanan halin da kasuwanci hade da tattalin ariziki duniya ke ciki. Jin sababin dabaru da hajojin da ake fataucinsu a kasashen duniya.

  • Lafiya

    Shirin dake tattanawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, Sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar.

  • Mahali

    Wayarda kan jama’a da ilmantar da su, game da shi’anin da ya shafi muhalli da yanayi. Yin bayanai dangane da batun gurbacewar yanayi tare da dumamarsa (Yanayi).

  • Masarautunmu

    Sarakuna a kasar Hausa da sauran yankunan kasashen Duniya suna da mutukar Muhimmaci ga al'ummarsu Akan haka ne kuma muka ga ya dace mu fito da wannan shirin domin farfado da darajarsu da muhimmacinsu ga ci gaban al'ummar domin babu wanda talaka yafi kusa da shi irin Sarkin garinsa kuma idan aka fahimci haka Sarakuna zasu taka rawa sosai domin sauya al'amurra a cikin kasa.

  • Mata Mazari

    Wannnan shiri ne akan Mata wanda ke tattauna fannoni daban-dabam da suka shafi ci gabansu, da matsalolin rayuwa ta bangaren jin dadi da rashinsa da suka shafi bangarorin Aure da ilimi da siyasa ...

  • Siyasa

    Shiri mai farin jini dake leka gidan kowa, dangane da siyasar duniya da irin wainar da ake toyawa akasashen. Bada dama ga Shugabanni da talakawansu su fadi abubuwan da ke gudana a yankunansu.

  • Tattaunawa

    Tattaunawa

    Shiri ne na musamman, da kan tattaunawa da bangarori daban-daban na Al’umma daga kowane kusurwa na fadin duniya, kan muhimman batutuwa, da suka shafi siyasa Tattalin’ariziki, ...

  • Waiwaye Adon Tafiya

    Waiwaye Adon Tafiya

    Shirin Waiwaye Adon Tafiya kan duba abubuwan da suka faru cikin mako, tare da gudanar da hirarraki. Shirin kan zo muko a ranakun Asabar da safe da kuma Lahadi da yamma.

  • Wasanni

    Labaran wasanni daga sassan duniya daban-daban na mintina biyu kan zo ma ku, bayan kun saurari labaran duniya, daga ranar littini zuwa Juma’a.

Close