
A ranar 21 ga watan Janairu ne aka fara gudanar da gasar cin kofin Afrika a kasashen Gabon da E/Guinea, inda kasashen Afrika 16 zasu haska a gasar, kuma wannan ita ce gasa mafi girma a Nahiyar Afrika. Bashir Ibrahim Idris, tare da bakinsa sun tattauna game da muhimmaci da tasirin gasar ga Afrika.
An fara gudanar da gasar ne a shekarar 1957, kuma tun a 1968 ake ci gaba da gudanar da gasar duk bayan shekaru biyu.
Kasashen Masar da sudan da kasar Habasha ne suka suka fara fafatawa a birnin Khartoum na kasar Sudan. Sai dai a lokacin kasar Afrika ta kudu ya kamata ace tana cikin gasar amma saboda rikicin cikin gida kasar ta fice gasar.
Sannu a hankali ne dai gasar ke ta smaun ci gaba, wajen samun kasashe dake shiga gasar wanda hakan ya bada damar aiwatar da wasannin share fage kafin shiga gasar.
A shekarar 1998 ne aka fara samun yawan kasashe 16 da suka shiga gasar, kuma tun daga lokacin yanzu ake rarraba rukunin kasashen gida hudu a zagayen farko.
Kasar Masar ce dai tafi kowace kasa a Nahiyar Afrika kafa tarihi a gasar inda ta lashe kofin gasar sau bakwai tun a zamanin da ake wa kasar da la’akabin Jamhuriyyar Tarrayyar Larabawa, Tsakanin 1958 zuwa 1971. kasashen Ghana da kamaru kuma sun samu nasarar lashe kofin gasar sau hudu ne.
A bana an samu hadin gwiwar kasashen Gabon da E/Guinea wadanda zasu dauki nauyin gasar.
sai dai a wannan karon manyan kasashe da suka yi fice a gasar zasu kasance ‘yan kallo musamman Najeriya da Masar mai rike da kofin da Kamaru da Afrika ta kudu da Algeria. Saboda kasa tsallakewa zuwa gasar.
A bana kuma an samun sabbin kasashen da suka samu shiga gasar karon farko da suka hada kasar Jamhuriyyar Nijar da Botawana da kuma E/Guinea da zata karbi bakuncin gasar.
Wannan gasa dai an shirya tane domin kara dankon zumunci da soyayya tsakanin kasashen Afrika, kuma gasa ce da ake bajakolin ‘yan wasan Afrika, inda kungiyoyin kwallon kafa a duniya ke bude idonsu domin cefanen ‘yan wasa.
Duk kasar ta lashe gasar dai ita ce ake danganta kasar da ta shahara a gasar fiye da kowa ce kasa a Afrika a fagen kwallon kafa.
Saboda kaucewa lokacin gudanar da gasar daidai da gasar cin kofin duniya a shekarar 2014 aka shirya sake gudanar da wata gasar irinta a badi.

Delicious
Digg
Facebook
Twitter
Yahoo!
Technorati






Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana