Isa ga babban shafi
MDD-IRAN

MDD na rike da jirgin agajin Iran mai zuwa Yeman

Majalisar dinkin duniya ta ce, ta na rike da Wani jirgin ruwa kasar Iran da ke dauke da kayayyakin agajin jin kai ga jama'ar Yemen bayan ya isa Djibouti, a inda jami'anta za su duba kayayyakin da ke cikinsa.

REUTERS/Stringer
Talla

Saudiya da kawayenta masu lugudan wuta kan 'yan tawayen Houthi a Yemen, sun zargin Iran da taimakawa 'yan tawayen da makamai, zargin da Iran ta musanta

Hukumar samar da abincin ta MDD ta ce ita za ta karasa da kayayyakin da suka kai ton 2500 na kayyakin abinci da magunguna da kuma sauran kayayyaki amfani.

Dakarun kawancen sun tsananta bincike akan jiragen ruwa da ke shiga Yemen domin hana shigar da makamai da za su fada hannun mayakan Houthi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.