Isa ga babban shafi
Indonesia

An kebe Bafaranshe cikin wadanda za a zartar wa hukunci a Indonesia

Kasar Indonesia ta kebe dan kasar Faransa daga cikin mutanen da za ta zartawar hukuncin kisa kan laifin safarar miyagun kwayu. An kebe Bafaransshe ne saboda matsin lamba da kasar ke fuskanta daga gwamnatin Faransa. Yanzu haka kuma an mika sauran mutanen guda 8 ‘Yan kasashen Brazil da Australia da Philippines da kuma Najeriya zuwa gidan yarin da za a bude ma su wuta.

Serge Atlaoui a hannun jami'an tsaron Indonesia
Serge Atlaoui a hannun jami'an tsaron Indonesia REUTERS/Beawiharta
Talla

Hukumomin Indonesia sun ce sun kebe Bafaranshen har zuwa wani lokaci saboda har yanzu batunsa yana kotu bayan ya daukaka kara.

Batun Serge Atlaoui ya haifar da takaddamar diflomasiya tsakanin Faransa da Indonesia.

Mahukuntan Faransa na yin matsi ga Indonesia domin neman ceto ran dan kasarta, a wajen madaukakiyar kotun kasar Indonesia bayan ta kara tabbatar da hukuncin kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.