Isa ga babban shafi
Cuba-Amurka

Cuba ta yaba da matakin Amurka

Kasar Cuba ta yaba da matakin da kasar Amurka ta dauka na cire ta daga cikin jerin sunayen kasashen da ke taimakawa ayyukan ta’addanci a duniya. Wannan na zuwa ne bayan shugabannin kasashen biyu sun gana a makon jiya a karon farko a Panama bayan sun shafe lokaci mai tsawo suna gaba.

Barack Obama na Amurka da Raul Castro na Cuba
Barack Obama na Amurka da Raul Castro na Cuba REUTERS
Talla

Kasar Cuba ta ce tun da farko bai kamata Amurka ta sanya ta a cikin sunayen kasashen da ke taimakawa ‘yan ta’addan ba, wanda ya kunshi kasashe irinsu Iran da Syria da Sudan.

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama ya amince ya cire sunan kasar Cuba daga cikin kasashe ma su taimakawa ta’addanci a duniya, matakin da ake ganin zai inganta huldar diflomasiyar kasahsen biyu.

Fadar shugaban ta ce Obama ya gabatarwa majalisar kasar bukatar yin haka, don amincewa da ita, da kuma bude ofisoshin jakadanci a Washington da Havana.

A makon jiya shugaba Obama ya gana da takwaransa Raul Castro a karon farko bayan sun kwashe shekaru sama da 50 suna takun saka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.