Hollande ya gana da Rauhani akan Nukiliya
Shugaban Faransa Francois Hollande, ya bukaci a samar da yarjejeniya mai inganci game da shirin Nukiliyar Kasar Iran, yayin da ya bayyana cewa kasar na da ‘yancin mallakar makamashi. Hollande, ya bayyana hakan ne, a wata tattaunawa da ya yi da Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani.
Wallafawa ranar:
Hollande ya jajirce cewa, Iran na da ‘yancin amfani da Nukiliya ta bangaren makamashi, lamarin da ya sa ya dage kan cewa, ya kamata a gaggauta cim ma yarjejeniya mai daurewa da kasar.
Ganawa tsakanin Holland da Rouhani, na zuwa ne, a daidai loakcin da aka dawo domin shiga zagayen karshe na tattaunawa tsakanin Iran da manayan kasashen duniya a kasar Switzerland, inda ake fatan cim ma yarjrjeniya.
Shugaban Kasar Iran, ya zanta da Firaministan Birtaniya David Cameron, ta wayar Tarho, inda ya bayyana ma sa cewa, Kasarsa na bukatar a cire ma ta dukkanin takunkuman da aka kakaba ma ta.
Tun a shekara ta 2013 ne, manyan kasashen duniya 6, da ke tattaunawa da Iran, suka bukaci ta yi watsi da wannan shiri da ake zargin cewa tana kokarin kera makaman nukiliya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu