An gano inda Jirgin Jamus ya fado
Kwararru tare da taimakon jami’an tsaro sun soma bincike a wurare da jirgin saman na kamfani Germanwings ya fadi a wani yankin kasar Faransa.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hadarin dai da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 150 da ke cikin jirgin da suka hada da Fasinjoji 144 da Ma'aikatan jirgin 6.
Shugaban kamfanin Jirage na Lufthansa, Carsten Spohr, ya bayyana cewa jirgin bashi da wata masala.
Kafin aukuwar hatsari jirgin ya kwashe tsawon shekaru 25 yana aiki.
Shugabannin kasashen Faransa, Jamus da kuma Spain, sun kai ziyara a kusa da inda lamarin ya faru, inda suka nuna alhinin su dangane da wannan hatsari da ake kallo a matsayin daya daga cikin mafi muni da ya faru a nahiyar Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu