Isa ga babban shafi
Faransa

Mutane 150 sun mutu a hadarin Jirgin Sama a Faransa

Mutane 150 ne, suka rasa rayukansu a wani hadarin jirgin saman kamfanin Germanwings na kasar Jamus, lamarin da ya auku a wani yanki da ke kudancin kasar Faransa

Bagiren tsaunukan da hadarin ya auku.
Bagiren tsaunukan da hadarin ya auku. La Provence/Twitter
Talla

Jirgin saman, kirar Airbus 320, ya baro birnin  Barcelona dake kasar spain inda ya nufi birnin Duesseldorf dake Jamus, yayinda ya gamu da hari a wani wuri cike da tsaunuka kudancin  faransa.

Kamfanin Jirgin saman ya tabbatar cewa akwai Fasinjoji 144 baya ga ma’aika 6 a cikin jirgin, kana akasarin matafiyan ‘Yan asalin kasar jamus ne.

Firaministan Spain, Mariano Rajoy, ya bayyana damuwarsa danganne da hadarin , inda yace, tuni sun hada kai da hukumomin kasashen Jamus da faransa dan gano musabbabin aukuwar hadarin.

Ana ta bangaren kuwa, Angela Markel, Shugabar Gwamnatin Jamus, ta bayyana cewa, za ta ziyarci bagiren aukuwan hadarin , inda kuma ta yi alkawarin zantawa da hukumomin yankin da hadarin ya ritsa da jirgin Saman.

Tuni dai Iyalan Fasinjojin suka yi cinkoso, a filin tashi da saukan jiragen sama na birnin Barcelona dake Spain, inda wasunsu ke ta zub da hawaye na rashin ‘Yan uwansu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.