An daba wa Jekadan Amurka wuka a Korea ta Kudu
Wani dan kishin kasa a kasar Korea ta Kudu ya daba wa Jakadan Amurka Mark Lippert wuka a fuska tare da yanka ma sa hannu a wani hari na nuna adawa da atisayen da sojin Amurka ke yi tare da sojojijn Koriya.
Wallafawa ranar:
Shaidun gani da ido sun ce mutumin ya boye wukarsa a hannun sa inda ya kutsa kai Cibiyar al’adun birnin Seoul, inda Jekadan ya ke tare da yanke shi a fuska da hannu, kafin jami’an tsaro su cafke shi.
Jekadan ya samu sauki bayan an garzaya da shi zuwa asibiti.
‘Yan Sandan sun bayyana mutumin a matsayin Kim Ki Jong mai shekaru 55 wanda ya taba jifar Jakadan Japan da dutse a shekarar 2010.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu