Isa ga babban shafi

'Yan sandan Mexico sun kama wani jagoram masu fataucin miyagun kwayoyi

‘Yan sandan kasar Mexico sun cafke wani jagoram masu fataucin miyagun kwayoyi mai suna police Servando Gomez, daya shahara wajen fita da miyagun kwayoyi zuwa Amurka. An kama Gomez wanda tsohon malamin makaranta ne da ake kira La Tuta, ba tare da anyi harbi ko sau daya ba, a lokacin daya fito daga wani gida a garin Morelia.An sami kama Gomez mai shekaru 49 ne, bayan da ‘yan sandan suka shafe watanni suna fakon shi, kuma tuni aka kai shi birnin Mexico City.Kamun Gomez ya nuna yadda hukumomin kasar ta Mexico suka kammala nade dukkan shugabannin gungunmasu fataucin miyagun kwayoyin kasar, dake aiki tamkar kungiyar asiri. 

'Yan Sandan Mexico, lokacin da suka kamo Servando Gomez
'Yan Sandan Mexico, lokacin da suka kamo Servando Gomez REUTERS/Edgard Garrido
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.