Isa ga babban shafi
Amurka

Kamfanonin Taba Sigari za su biya diyya a Amurka

Wasu Manyan kamfanonin tabar sigari guda uku na Amurka da suka hada da Philip Morris da RJ Reynolds da Lorillard sun amince su biya diyyar Dala miliyan 100 kan wasu kararaki sama da 400 da ke kalubalantar yadda tabarsu ta haifar da rashin lafiya ga masu zukar ta.

Tabar Zamani
Tabar Zamani gettyimages
Talla

Wani alkali a Jihar Florida ne ya umurci kamfanonin tabar su biya diyyar sakamakon karar da wasu ma su zukar tabar da kuma iyalansu suka shigar.

Dangane da hukuncin kamfanin Philip Morris da ke yin tabar Marlboro, da RJ Reynolds da kuma Lorillard za su hada hannu don biyan diyyar ta dala miliyan 100.

Daya daga cikin lauyoyin ma su karar Robert Nelson, ya bayayna farin cikinsu da hukuncin, inda ya ke cewar diyyar za ta taimaka wa wadanda suke karewa wadanda akasarin su masu yawan shekaru ne.

Sai dai hukuncin ya tsaya ne kawai kan mutanen da suka shigar da kara.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.