Isa ga babban shafi
AU-Zimbabwe

Shugaba Robert Mugabe sabon shugaban kungiyar AU

Shugaba Mugabe wanda ya kasance shugaban da kasashen Nahiyar Turai ke harara tun bayan da ya samu shugabancin kasar Zimbabwe a shekarar 1980, ya kasance shugaban kungiyar tarayyar Afrika ne, bayan da shugabannin Afrika mahalarta taron kungiyar kasashen suka saka masa kuri’ar amincewa a kasar Habasha.Mugabe mai shekaru akalla 90, ya bayyanawa shugabannin kasashen cewar ya amince da zaben da suka yi masa

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Da wannan nasarra da ya samu, Mugabe zai yi kyakkyawan jagoranci ta hanyar sauke nauyin da aka dora masa.
Akasarin shugabanin kasahen Afrika suna goyon bayan Mugabe a matsayin sabon shugaban kungiyar tarrayar Afrika ta AU.

Sai dai shugaba Mugabe a cikin kasar sa yana fuskantar suka akan yanda ‘yan adawa ke zargin sa da murkushe su domin shifnida mulkinsa ba tare da wani tarnaki ba, musamman lura da yanda ya yita samun nasara a zabubukan kasar dama na shugaban kasar da aka yi sau 3 a zimbabwe.

A Baara dai shugaba Mugabe ya kauracewa taron kungiyar kasashen Afrika ne, bayan da aka bashi takardar gayyata .

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.