Isa ga babban shafi

Kasashen duniya suna sukar Turkiyya kan rashin kare hakkin dan Adam

Kasar Turkiyya na fuskantar suka ainun daga majalisra dunkin Duniya kan zargin da ake mata na keta hakkin bil’adama ta hanyar gallazawa mutane, da kuma dukan kawo wuka da ‘yan sandan kasar ke yiwa mutane masu zanga-zanga.Hukumar kula da hakkin bil’adama ta Majalisar dinkin Duniya ta ce a halin da ake ciki, wannan batu na daga cikin ababen da ta maidawa hankali, musamman yadda kasar ta turkiyya ke saka wa ma’aikatan kafafen watsa labarai tkunkumin hana fadar albarkacin baki.Wakilin kasar Amurka a hukumarkare hakkin dan Adam ta duniya Keith Harper, yace wasu daga cikin matakan da hukumomin na Turkiyya ke dauka sun hada da tantance irin labarun da ‘yan jarida ke amfani dasu.Kalaman Harper, dake nuna matukar damuwar hukumar kan wadannan matakan, na zuwa ne a daidai lokacin da aka yi nazarin matakan kare hakkin dan Adam a kasar ta Turkiyya.Sai dai kasar ta Turkiyya ta mayar da martani kan wannan zargin, inda tace tana daukar kwararan matakai, don kula hakkokin jama’a. 

Fraiministan kasar Turkiyya, Ahmet Davutoglu
Fraiministan kasar Turkiyya, Ahmet Davutoglu REUTERS/Stringer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.