Isa ga babban shafi
Amurka-Cuba

Amurka ta tattauna da Cuba

A yau Alhamis an shiga rana ta biyu a ci gaba da tattaunawa tsakanin wakilan Amurka da na Cuba a birnin Havana, taron da ake kallo a matsayin muhimmi wajen sake dawo da huldar diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu. Majiyoyi sun ce tattaunawar da bangarorin biyu suka yi a jiya ta yi matukar armashi, kuma akwai yiyuwar kasashen su dauki matakin sake buda ofisoshin jakadancinsu a karshen wannan taro.

Josefina Vidal da Roberta Jacobson Jami'an diflomasiyar Amurka da cuba
Josefina Vidal da Roberta Jacobson Jami'an diflomasiyar Amurka da cuba Reuters
Talla

A cikin watan Disemba ne Shugaba Barack Obama ya bayar da sanarwar kawo karshen takun sakan da aka shafe shekaru da dama ana yi tsakanin Amurka da Cuba. Obama da Castro sun amince su tattauna domin inganta hulda tsakanin Cuba da Amurka.

Hukumomin birnin Washington sun dauki tsawon shekaru kusan 50 suna mayar da Cuba saniyar ware a harkokin diplomasiyyar kasashen duniya.

Shugaba Raul Castro ya bukaci Amurka ta janye takunkumin da ta kakabawa Cuba don ba Amurkawa damar yin walwala a cikin kasar.

A baya dai ba kowa ake bari ya je Cuba daga Amurka ba, face mutanen da suka hada da ‘yan jarida da malaman makaranta da jami’an gwamnati da wadanda ke da ‘yan uwa a can, amma yanzu Amurakawa da dama za su samu izinin shiga Cuba.

Wannan sauyin, zai bai wa ‘yan kasar Cuba da ke zaune a Amurka damar aika wa ‘yan uwansu kudade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.