Isa ga babban shafi
Libya

Gwamnatin adawa a Libya ta bukaci ‘yan kasashen waje su dawo Tripoli

Gwamnatin da ke ikirarin iko da kasar Libya, ta yi kira ga jami’an diflomasiya da kamfanonin kasashen waje su koma birnin Tripoli, don ci gaba da gudanar da harkokinsu. Gwamnatin, da ke samun goyon bayan mayakan Islaman kasar ta yi alkawarin bayar da kariya ga ‘yan kasshen waje da ke kasar.

Sojan mayakan sa-kai na musayar wuta a birnin Tripoli na Libya
Sojan mayakan sa-kai na musayar wuta a birnin Tripoli na Libya REUTERS
Talla

Gwamnatin, ta yi alkawarin kare ‘yan kasashen wajen da ke Libya, duk da wani harin da aka kai gidan jakadan kasar Switzerland.

Gwamnatin da ke karkashin Omar al-Hassi, tace za a bai wa ‘yan kasashen waje kariya daidai da yadda za a bai wa ‘yan kasar ta Libya.

Shekaru uku, bayan da kungiyar tsaro ta NATO ta jagoranci sojojin da suka taimaka aka hambarar da gwamnatin marigayi Kanal Ghaddafi, har yanzu kasar Libya na fama da ‘yan bindigan da ke cin karensu ba babbaka, inda suke amfani da manyan makaman yaki.

A watan Agusta mayakan Fajr Libya, suka karbe ikon birnin Tripoli, inda suka nada Hassi a matsayin Firaminista.

Sai dai yanzu haka wannan gwamnatin na fuskantar kalubale daga gwamnati Firaminista Abdullah al-Thani, mai samun goyon bayan kasashen duniya, da aka kafa bayan zaben ‘yan majalisu a watan Yuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.