Isa ga babban shafi
Faransa-Afghanistan

Sojojin Faransa za su fice Afghanistan

A karshen watan nan na Disemba ne, sauran dakarun Faransa da suka rage zasu fice daga Afghanistan. Wannan kuma shi zai kawo karshen yakin da dakarun NATO ke yi tsawon shekaru 13 a cikin kasar ta Afghanistan.

Dakarun Faransa a kasar Chadi
Dakarun Faransa a kasar Chadi REUTERS
Talla

A ranar 31 ga watan Disemba ne ma’aikatar tsaron Faransa tace sauran dakarunta 150 da ke cikin kawancen NATO zasu fice daga Afghanistan.

Dama dai a wannan karshen watan ne na Disemba kungiyar kawancen tsaro ta NATO za ta kammala yakin da ta ke yi da Taliban a Afghanistan.

Faransa dakaru 70,000 ne ta tura Afghanistan, kuma tun soma yakin Sojojinta 86 aka kashe tare da raunata 700.

Amma akwai dakaru kimanin 12,500 da za su rage a cikin Afghanistan yawancinsu Sojojin Amurka wadanda zasu ba dakarun kasar horo domin ci gaba da tafiyar da tsaro a cikin kasar.

Sai dai kuma ana fargabar ko sojojin Afghanistan na iya tafiyar da sha’anin tsaro a kasar bayan ficewar NATO saboda kazancewar hare haren mayakan Taliban a cikin kasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.