Isa ga babban shafi
Amurka-Cuba

Amurka ta shirya da Cuba

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayar da sanarwar kawo karshen takun sakan da aka shafe shekaru da dama ana yi tsakanin Amurka da Cuba. Obama da Castro sun amince su tattauna domin inganta hulda tsakanin Cuba da Amurka.

Masu zanga-zangar adawa da shirin farfado da huldar Cuba da Amurka a Miami
Masu zanga-zangar adawa da shirin farfado da huldar Cuba da Amurka a Miami REUTERS/Javier Galeano
Talla

Hukumomin birnin Washington sun dauki tsawon shekaru kusan 50 suna mayar da Cuba saniyar ware a harkokin diplomasiyyar kasashen duniya.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yaba da matakin da kasashen suka dauka na farfado da da huldar diflomasiya a tsakaninsu, yana mai yin alkawarin cewar majalisar za ta taimaka.

Ban ya shaidawa manema labarai farin cikin majalisar na kawo karshen takun-sakar da aka kwashe sama da shekaru 50 ana yi inda ya yabawa shugaba Barack Obama da Raul Castro a kokarin da suka yi na ganin an samu ci gaba.

Shugaba Raul Castro ya bukaci Amurka ta janye takunkumin da ta kakabawa Cuba don ba Amurkawa damar yin walwala a cikin kasar.

Cikin sauye sauyen da za a gani sakamakon wannan matakin, shugaba Obama zai bai wa ma’aikatar harkokin waje umarnin dawo da dangantakar diflomasiyya tsakanin Amurka da kasar, mai bin tsarin Kwaminisanci.

A baya dai ba kowa ake bari ya je Cuba daga Amurka ba, face mutanen da suka hada da ‘yan jarida da malaman makaranta da jami’an gwamnati da wadanda ke da ‘yan uwa a can, amma yanzu Amurakawa da dama za su samu izinin shiga Cuba.

Wannan sauyin, zai bai wa ‘yan kasar Cuba da ke zaune a Amurka damar aika wa ‘yan uwansu kudade.

A shekarar 1982 Amurka ta ayyana Cuba a matsayin mai goyon bayan ayyukan ta’addanci, inda ta zargi hukumomin birnin Havana da bada mafaka ga ‘yan tawayen kasar Colombia, amma yanzu Shugaba Obama ya bayar da umarnin sake nazarin wannan, kuma ana sa rai fito da rahoto cikin watanni 6 masu zuwa.

Nan gaba kasashen biyu za su ci gaba da tattaunawa domin warware sabanin da ke tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.