‘Yan Jaridu 66 aka yi wa kisan gilla a 2014
Kungiyar da ke sa ido kan ayyukan ‘Yan Jarida wato Reporters Without Borders tace ‘yan Jaridu 66 aka yi wa kisan gilla a cikin watanni 12 da suka gabata. A cikin rahotan da kungiyar ta gabatar ta bayyana fille kan Jamse Foley da Steven Sotloff da mayakan IS suka yi a Iraqi a matsayin irin hadarin da ke tattare da aikin dauko rahoto a inda ake samun tashin hankali.
Wallafawa ranar:
Kungiyar tace yadda aka kashe wadannan ‘yan Jaridu biyu ya sabon abu ne aka saba gani a duniya.
Kungiyar ta kuma bayyana cewar an yi garkuwa da ‘Yan Jarida 119. 33 a Ukraine, 29 a Libya da kuma 27 a Syria.
Kungiyar tace jimillar ‘Yan Jarida 720 aka kashe tun 2005 zuwa yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu