Isa ga babban shafi
MDD

Amfani da karfin Soji ba zai magance ta’addanci ba -Ban Ki-moon

Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke nazarin daukar matakan dakile kwararar mayaka daga kasashen waje zuwa Iraqi da Syria, Sakataren Majalisar Ban Ki-moon ya yi gargadin kaucewa yin amfani da karfin Soji wajen murkushe masu tsautstsauran ra’ayin addinin Islama, tare da yin kira ga gwamnatoci wajen kaucewa keta hakkin bil’adama da sunan farautar ‘Yan ta’adda.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon REUTERS/Adrees Latif
Talla

Ban Ki-moon ya fadawa kwamitin tsaro cewa MDD na nazarin daukar matakan da suka dace na tunkarar ta’addanci a duniya, ta hanyar gano tushen al’amarin.

Ban ya yi gargadi ga kasashen duniya su kauracewa keta hakkin mutane da sunan yaki da ta’addanci.

Ban Ki-moon ya yi wannan gargadin ne a zaman taron Kwamitin tsaro na MDD akan nazarin dakile yadda mayaka daga kasashen Turai ke kwarara zuwa Iraqi da Syria domin marawa Mayakan IS baya.

A zaman taron, Ministar harakokin wajen Australia Julie Bishop ta bukaci a samar da kwamiti da zai wayar wa mutane kai akan ayyukan ta’addanci musamman a kafafe sadarwa na Intanet.

Daruruwan mayaka ne dai daga kasashen waje suka je yaki Syria da Iraqi, inda a makon nan wasu Faransawa guda biyu suka fito a hoton bidiyon da Mayakan IS suka fille kan wani Ba’amurke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.