An ga Bafarashe cikin Mayakan IS
Masu bincike a Faransa sun gano wani Bafaranshe na biyu a cikin faifan bidiyon da ke nuna yadda kungiyar IS suka fille kan wani Ba’amurke da kuma sojojin Syria 18 a karshen makon da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Wannan dai na mai kara tabbatar da cewa akwai ‘Yan asalin kasashen Yammacin duniya da dama da ke taka rawa cikin kungiyoyin da ke da’awar jihadi a sassa daban na duniya.
Kasashen Turai da dama ne dai ke ci gaba da gudanar da bincike a game da faifan bidiyo da kungiyar IS ta fitar a karshen makon da ya gabata, bayan da aka fahinci cewa daga cikin wadanda ke fille kawunan har da Faransawa biyu da aka bayyana sunayensu a mastayin Maxime Hauchard da Michael Dos Santos.
Dukkaninsu an ce kiristoci ne amma suka rungumi addinin musulunci kafin a gano cewa tuni suka isa Syria domin Jihadi.
A can baya ma, lokacin da mayakan jihadin suka fillewa wasu ‘yan jaridun Amurka biyu kawuna tare da nuna hakan a yanar gizo, hukumomi a Birtaniya sun tabbatar da cewa daya daga cikin masu fille kawunan cikakken Bature Ingile ne.
A kasar Belgium ma ana gudanar da aiki domin tantance wani mutum da ya fito a hoton shekaran jiya, wanda ake zaton cewa dan kasar ne.
Tun daga lokacin da yaki ya barke a Syria ne aka soma samun kwararar ‘yan asalin kasashen Yamma zuwa Yankin Gabas ta Tsakiya, kuma akasarinsu domin jihadi, lamarin da ya haifar da damuwa a tsakanin al’ummomin wadannan kasashe.
Sai dai babban abin tambaya a nan shi ne, ko me ke kara kwadaitawa Turawan daura damarar zuwa jihadi a kasashen Syria da Iraki da kuma sauran bangarori na duniya?
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu