Yawan mutanen dake kamuwa da annobar cutar Ebola zai karu da mutane dubu 10 a kowane mako inji WHO
Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa abu ne mai yiyuwa, yawan mutanen da ke kamuwa da cutar Ebola ya zarta dubu 10 a kowane mako matukar dai kasashen duniya ba su dauki matakan da suka wajaba ba, domin tunkarar wannan annoba ba.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Har ila yau hukumar lafiyar ta bayyana cewa yawan mutanen da ke mutuwa sakamakon kamuwa da cutar Ebola sun kai kashi 70 cikin dari a kasashen 3 da cutar ta bulla a cikinsu dake yankin yammacin Afrika, kamar yadda Bruce Aylward, mataimakin darakatan hukumar lafiya ta Majalisar DD Ya sanar a jiya talata
Yanzu haka dai za a iya cewa cutar ta Ebola ta kusa zama annobar daukacin kasashen duniya sakamakon mutuwar wani jami’in Majalisar DD da ya kamu da cutar, bayan kwantar da shi a wani asibiti dake kasar Jamus a jiya talata, yan sa’oi bayan soma gudanar da zaman taron kwamitin tsaro na MDD, kan yaki da cutar ta Ebola, wace ta yi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu 4 a yankin yammacin Afrika
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu