Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya zata shiga yaki da yan kungiyar ISIS

KASAR Turkiya ta tutra tankunan yaki kan iyakarta da Syria a ya yin da Yan Majalisunta ke tabka mahawara kan daukar matakin soji akan mayakan jahadin kungiyar ISIS na kasashen Iraki da Syria.

Talla

Rahotanni sun ce sojin Turkiya sun girke tankunna yaki da makaman roka a garin Mursitpinar wanda ke kusa da garin Kurdawan Ain al Arab, bayan wasu jerin harsasai sun samu kauyukan dake cikin kasar ta Turkiya.

Kakakin Majalisar kasar Cemil Cicek yace a yau talata suke saran gwamnati ta gabatar da kudirin daukar matakin soji.

Baya ga kasar ta Turkiya kasashen larabawa da dama ne suka dafawa kasar Amruka da kawayenta baya wajen yakar yan kungiyar mujahidan dake fafatukar kafa daular musulunci a kasashen Iraki da Siriya ISIS

Kasashen dais un hada da Saudiya, Imarat Arba, Qatar, Jordan da kuma Bahren
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.