Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Dimamar yanayi na kalubalantar Duniya inji taron majalisar dinkin Duniya

Shugabannin kasashen Duniya da suka taru a zauran majalisar dinkin Duniya a birnin New York na kasar Amurka, sun jaddada kudurinsu na fuskantar kalu-balen da dimamar yanayi ke haifar wa, inda suka sha alwashin daukan matakin magance matsalar

uni.edu
Talla

Majalisan dinkin Duniyan na kokarin tabbatar da samun sassauci dangane da yanayin zafin kasa inda ta bayyana cewa za ta yi zama na karshe a birnin Paris na Faransa a shekara mai zuwa.

kasashen Duniyar dai za su sa hannu bisa yarjejeniya ta yadda za,a kawar da wannan kalu-bale na dimamar yanayi, yayin da jama,a daga kasashe daban daban suka yi zanga zangar lumana, suna kiran gwamnatoci da su gaggauta magance wannan matsalar wadda ke sanadiyar ambaliyan ruwan Teku da Fari da kuma guguwar Iska.

Wani mai lura da al,amuran taron majalisan dinkin duniyan, Mr. Meyer ya bayyana cewa, shuwagabannin kasashen duniyar da suka taru a birnin New York, za su samu hadin kai dan ganin sun cimma burinsu na taronsu na gaba da za,a yi a a Faris shekara mai zuwa, ya kuma tabbatar da cewa baza’a sake samun rashin jituwa ba kamar yadda ta faru a taron Copenhagen da aka yi a shekara ta 2009.

A cewar Shugaban Kasar faransa, Fracios Hollande ya bayyana cewa taron da za’a yi kwatan kwacinsa a Paris Shekara mai zuwa, zai haifar da da mai Ido sannan yayi kira da babban murya inda yace, dimamar yanayi nayin barazana ga tsaro da kuma zaman lafiyar Duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.