Australiya zata tura dakaru 600 don yakar 'yan kungiyar IS a Iraqi
Yau Lahadi kasar Australiya ta bayyana aniyar tura dakaru 600 zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, don tallafawa kokarin da Amurka ke jagoranta, na yakar ‘yan kungiyar IS a gabas ta tsakiya. Sanarwar da Fraiminista Tony Abbott ya bayar na zuwa ne kwanaki 2, bayan hukumomin birnin Canberra sun kara yawan fargabar harin ta’addanci da za a iya kaiwa Australiya, daga matsakaicin mataki zuwa babban mataki, lamarin da ke nuna za a iya kai mata hari a kowane lokaci.Shugaban yace kasar ta tura sojan sama 400, da na kasa 200, bayan Amurka ta nemi taimako a kokarin da ake yi, na kawar da kungiyar ta IS.Mr. Abbott yace dakarun kasar zasu mayar da hankali ne kan kasar Iraqi, amma banda Syria.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: