Isa ga babban shafi
Iraqi-Faransa

Hollande ya kai ziyara Iraqi

Shugaba Francois Hollande ya bayyana nuna goyon bayan Faransa ga sabuwar Gwamnatin Iraqi a yakin da take yi da ‘yan tawayen kungiyar IS da suka kwace ikon wasu yankuna a kasar da Syria. Hollande shi ne shugaban kasa na farko da ya kai ziyara a Iraqi tun kafa sabuwar gwamnati.

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande REUTERS/Laurent Capmas
Talla

Shugaba Hollande yace Iraqi zata samu goyon bayan Faransa a lokacin da suke ganawa da Fuad Masum shugaban Iraqi.

Jirgin shugaban na na Faransa ya isa Iraqi ne dauke da kayan agaji, kuma cikin tawagar shugaban akwai Ministan tsaro, Jean-Yves Le Drian, da Ministan harkokin waje Laurent Fabius.

Tuni kasar Amurka ta kaddamar da hare hare da jiragen sama akan Mayakan IS amma Faransa da Birtaniya na ja da baya ga matakin

A ranar 15 ga wannan watan na Satumba, Faransa za ta karbi bakuncin taron kasashen duniya kan rikicin na Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.