Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Amurka na neman hadin kan kasashe don tunkarar 'yan kungiyar IS

Amurka ta nemi hadin kan kasashen duniya, don tunkarar abinda ta kira kisan kare dangi da kungiyar IS ta shirya a Syria da arewacin Iraqi. Sakataren harkokin wajen Amukan John Kerry, yace shugaba Barak Obama zai gabatar da hanyoyin da za a bi, don kawo karshen ayyukan kungiyar, a wajen taron kwatinin Tsaro na MDD, a watan Satumba mai zuwa, lokacin da Amurka zata karbi ragamar shugabancin kwamitin.Yayin da ake shirin yin taron kungiyar tsaro ta NATO a mako mai zuwa, Kerry yace shi da Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel, zasu gana da takwarorinsu na kasashen Turai, don duba yuwuwar samun tallafi. 

Shugaban Amurka, Barack Obama
Shugaban Amurka, Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.