Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Gaza: Isra’ila ta yi watsi da ikirarin Hamas

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yace Isra’ila ta samu nasara a kwanaki 50 da aka kwashe Sojojinta na ruwan wuta a Zirin Gaza tare da yin watsi da ikirarin Kungiyar Hamas akan Falasdinawa ba su samu ko da guda daga cikin bukatunsu ba a yarjejeniyar tsagaita wuta da suka amince.

Prime Ministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu
Prime Ministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu REUTERS/Nir Elias
Talla

A wata hira da manema labarai kan yakin da Isra’ila ta gwabza da kungiyar Hamas, Firaminista Benjamin Netanyahu yace Hamas ta smau koma baya sabanin nasarar da ta ke ikrarin samu.

Natenyahu yace sun ruguza Kungiyar Hamas kuma ba ta samu biyan bukata koda guda daga cikin sharuddan da ta gabatar ba.

Akalla Falasdinawa 2,140 ne Isra’ila ta kashe yawancinsu fararen hula yayin da kuma Sojojin kasar 64 suka mutu.

Netanyahu kuma yace sun ruguza hanyoyin karkashin kasa kusan guda 1,000 da Hamas ke cilla rokoki tare da kashe wasu shugabannin kungiyar.

Tun a yammacin Talata ne dai bangarorin biyu suka tsagaita wuta karkashin yarjejeniyar da suka amince a kasar Masar, amma akwai wasu bukatu da bangarorin biyu ba su amince ba da suka hada da sakin fursunoni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.