Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Amurka tace kashe dan jaridanta a Iraqi aikin ta'addanci ne

Amurka tace fille kan da jaridan kasar James Foley, da aka yi a Iraqi harin ta’addanci ne, matakin da zai bata damar yin fito na fito da mayakan kungiyar IS a gabashin kasar ta Iraqi. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ‘yan bindiga ‘Yan Shi’a suka kashe mutane 70 a wani masallacin mabiya Sunni a lardin Diyala.Harin mai kama da ramuwar gayya, zai iya sake fusata mabiya Sunni larabawa, marasa rinjaye a kasar ta Iraqi, tare da kawo cikar a kokarin kawo karshen rikicin kasar ta hanyar jawo su, su shiga a dama dasu a gwamnatin kasar, da ‘Yan Shi’a ke jagoranta. 

Dan Jarida James Foley, da aka kashe a Iraqi.
Dan Jarida James Foley, da aka kashe a Iraqi. REUTERS/Louafi Larbi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.